DSS ta Kama Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Kingsley Obiora

 

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta kama Kingsley Obiora, mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) mai kula da manufofin tattalin arziki.

Koda dai rundunar tsaron sirrin bata tabbatar da lamarin ba amma majiyoyi na kusa sun tabbatar da cewa jami’an DSS na ci gaba da tsitsiye Obiora a halin yanzu.

Kamun Obiora na da alaka da zargin barnar da aka tafka a karkashin Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan CBN.

Rahotanni da ke zuwa mana sun ce jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun tsare mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Kingsley Obiora.

Tsare shi da jami’an tsaron suka yi ya jefa babban bankin kasar a cikin fargaba yayin da yawancin ma’aikatan suka rude.

Wata majiya ta tsaro ta tabbatarwa jaridar The Nation batun tsare Obiora a ranar Juma’a, 1 ga watan Satumba.

Yayin da yake tabbatar da kamun nasa, majiyar ta kuma tabbatar da cewa ba shi kadai ne jami’in CBN da ke tsare a hannun DSS ba amma ya ki bayyana sunayen sauran, New Telegraph ta rahoto.

A halin da ake ciki, kakakin rundunar DSS, Peter Afunanya bai riga ya tabbatar da ci gaban ba.

Sauran abubuwan da ke da nasaba da kamun da ake zargin an yi wa Obiora

Ana ta yadawa cewa Kingsley Obiora yana tsare a hannun hukumar DSS ne bisa umarnin kwamitin bincike na musamman da shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa don binciken mulkin dakataccen gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele.

An yi zargin cewa kwamitin bincike na musamman karkashin jagorancin Jim Obaze na matsawa Obiora don ya tsaya a matsayin shaida a kan dakataccen shugaban babban bankin.

Kwamitin yana matsawa Obiora, mai ba da shawara a baya, da ya ba da shaida kan Emefiele. Yayin da hukumomi ke yi wa wasu manyan jami’an bankin tambayoyi, ba a zargin Dr Obiora da zamba ko sata.

Sai dai kuma, majiyoyi sun bayyana cewa kwamitin ya dage cewa ya san fiye da abun da yake fadi game da mulkin Emefiele, koda dai ya ba da hadin kai sosai duk da kokarin da suka yi na kai shi bango.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com