A bar Gwamnatin Buhari ta Cigaba da ci – in ji Rarara

 

Dauda Adamu Kahutu zai so Muhammadu Buhari ya yi ta mulki har zuwa 2027.

Babban mawakin yana ganin zai yi kyau a karawa Buhari shekaru hudu ko biyar.

A wata hira da aka yi da shi, Rarara ya fadi sirrin kaunar da yake yi wa Buhari.

Katsina – Dauda Adamu wanda aka fi sani da Rarara, ya yi hira ta musamman da BBC Hausa, inda ya tabo batutuwan siyasa da yadda yake shirya wakoki.

Shahararren mawakin ya bayyana cewa akwai bukatar a bar Muhammadu Buhari ya cigaba da mulki.

Da yake bayanin rayuwarsa, an ji cewa an haifi fitaccen mawakin ne a garin Kahutu, karamar hukumar Danja, a jahar Katsina, ya kuma dade a waka.

A wannan hira da aka yi da mawakin, aka kuma wallafa a ranar 24 ga watan Oktoba, 2021, yace zai yi kyau a kyale Buhari ya karasa ayyukan da ya fara.

A bar Gwamnatin Buhari ta cigaba da ci

“Idan Buhari ya gama ka’idojin mulkinsa, idan ta ni za a bi, da za ayi shawara da ni, akwai bukatar a kara masa shekaru hudu ko biyar.” – Dauda Rarara

“Saboda abubuwan da ya turo su gama, ya kammala su.Amma wannan nawa ra’ayin kenan.”

“Amma na san idan na fito da abin da na gani, su ma za su hau kan wannan layin.”

Meyasa Rarara yake yi wa Buhari waka?

Har ila yau, da aka tambayi Dauda Adamu Kahutu Rarara dalilin da ya sa yake yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari waka, sai yace gaskiyarsa.

“Tun da nake karami sosai ake ce mani Buhari ne mai gaskiya, har yau ban ji kishiyar haka ba.” – Rarara

“Ba nayi Buhari don ya bani wani abu ba, ba na yi shi domin in samu kudi ba. Ba na yi shi domin in samu mukami ba. Na yi domin yana kishin kasa ta” – Rarara.

Mawakin ya bayyana cewa ya yi wa Buhari wakoki har 66, amma a ciki yace ‘Sai Baba Buhari’ ce bakandamiyarsa, duk da an fi sanin shi da ‘Masu gudu, su gudu.’

Rarara ya shaidawa BBC Hausa cewa akwai wanda ya taba yi masa tayin Naira miliyan 500 domin ya daina yi wa Buhari waka, amma ya ki karbar wannan tayi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here