Rabi’u Kwankwaso: Gwamnatin Kano ta yi wa Tsohon Gwamna Karamci

Gwamnatin Jihar Kano ta yi sabbin nade nade a masarautar karamar hukumar Karaye.

Wani jami’i daga karamar hukumar Karaye ya bayyana cewa sabbin wadanda aka yi wa nadin za su fara aiki a ranar Juma’a 27 ga watan Nuwamba.

A halin yanzu jihar Kano tana da masarautu guda biyar da sarakuna masu daraja ta daya suke jagoranta.

An nada Musa Saleh Kwankwaso, mahaifin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan Kano a matsayin dan majalisar nadin sarakuna a masarautar Karaye ta Jihar Kano.

Mai magana da yawun masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis 26 ga watan Nuwamban kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Gunduwawa ya ce a ranar Juma’a 27 ga watan Nuwamba ne za a rantsar da Saleh Kwankwaso wadda dama ke rike da sarautar ‘Makaman Karaye’ a matsayin dan majalisar sarki.

Masarautar Karaye na cikin sabbin masarautu hudu da gwamnatin Jihar Kano ta kirkira karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje a ranar 5 ga watan Disamban 2019.

Dokar da Ganduje ya rattaba wa hannu ta bada damar bawa sarakunan hudu matsayin daraja ta farko wadda suka hada ba Bichi, Karaye, Rano da Gaya.

Jim kadan bayan kirkirar sabbin masarautun ne aka tsige gwamnan Kano, Muhammadu Sanusi II.

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso yana daga cikin wadanda ba su goyi bayan kirkirar sabbin masarautun ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here