Mun Kunsan Kawo Karshen ‘Yan ta’adda – John Enenche

Kwanan nan ta’addanci zai zo karshe a Najeriya, cewar kakakin rundunar sojin Najeriya, John Enenche.

Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, yayin gabatar da jawabi game da nasarorin sojoji a Abuja.

A cewarsa, a ranar 21 ga watan Nuwamba, rundunar soji ta ragargaji ‘yan ta’addan arewa maso yamma.

Hedkwatar tsaro ta tabbatar da yadda kwanan nan za ta kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin taron bayar da bayani a kan ayyukan rundunar soji.

A cewarsa, ta yadda sojoji suke ragargazar ‘yan ta’adda, kwanan nan za su zama tarihi.

Ya kara da cewa: “Rundunar Operation Hadarin Daji da sauran rundunoni masu taimakonsu suna ragargazar ‘yan ta’addan arewa maso yammacin kasar nan kuma suna samun nasarori na ban mamaki.

“Jaruman sojojin suna ratsa dazuzzuka, lungu da sako wurin neman ‘yan ta’adda a maboyarsu.

“A ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, rundunar Operation Accord sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga 2 har suka samo bindigogi kirar AK47 guda 2.

“Sannan a ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, rundunar ta je sintiri wuraren kauyen Gobirawa suka yi kacibus da ‘yan bindigan.

A karon battar, sun kashe ‘yan bindiga 6, sannan suka samu bindigogi 2 kirar AK 47, kananun bindigogi 3 da babura 2.

“Sannan bayan rundunar sun yi amfani da dabara ta musamman, sun gano wasu mutane masu hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba guda 11.

“Rundunar sun tura duk wadanda ake zargin ofishin ‘yan sanda don a cigaba da bincikarsu.”

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here