Dalilin Komawata APC – Sanata Elisha Abbo

 

Sanata Ishaku Abbo na jihar Adamawa ya canja sheka, daga PDP zuwa APC.

A cewarsa, da a cikin duhu yake, amma canja shekarsa yanzu ya koma haske.

Ya kara da cewa, ya koma jam’iyyar APC ne saboda jam’iyyar adalci ce.

Sanata Ishaku Abbo, mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana canja shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya ce ya bar jam’iyyar PDP ne don kowa ya san shi.

Legit.ng ta tattaro bayanan yadda dan majalisar da aka zaba a jam’iyyar PDP ya koma APC a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba.

Sai da sanatan suka yi wani taro da shugaban kwamitin rikon kwarya, Gwamna Mai Mala Buni, a babban ofishin jam’iyyar a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba a Abuja.

Inda Abbo ya sanar da manema labarai cewa ya bar jam’iyyar PDP ne saboda zalunci. Sannan ya bar duhu ya koma haske.A cewarsa, babban dalilin shiga siyasa shine yi wa al’umma aiki da taimakon talakawa da yi musu adalci.

“Ina son jam’iyyar APC saboda ta adalai ce. Da izinin Ubangiji jihar Adamawa za ta bunkasa a 2023, kuma za ta samu zabi na kwarai,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here