Gwamnatin Jahar Kano ta Zabtare Albashin Ma’aikata
Gwamnatin jahar Kano ta sanar da daina biyan ma’aikatanta karancin albashin N30,000.
Jihar ta gaggauta komawa biyan karancin albashin zuwa N18,000 a ranar 6 ga watan Janairu.
Gwamnatin ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan karayar tattalin arzikin da aka shiga saboda Covid-19.
Annobar korona ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin jihohi da dama na Najeriya ballantana jihar Kano.
Read Also:
Hakan yasa gwamnatin jihar Kano ta sanar da komawa biyan ma’aikatanta karancin albashin N18,000 a maimakon N30,000 da ta fara bayan boren da kungiyar kwadago tayi, The Cable ta ruwaito.
A yayin tabbatar da wannan cigaban, mai magana da yawun Gwamna Umaru Ganduje, Salihu Tanko-Yakasai, ya ce halin da kasar nan ta shiga sakamakon annobar korona ce ta saka hakan.
Ya ce: “Gwamnatin jihar ta koma biyan tsohon karancin albashi saboda halin da ta shiga. Abinda muke samu a matsayin gwamnati yanzu ya ragu kuma ba za mu iya cigaba da biyan N30,000 ba a matsayin karancin albashin.”
Amma kuma, ma’aikatan gwamnatin da ke jihar sun jajanta yadda gwamnatin jihar bata bada wata sanarwa ba kafin ta fara zabtare musu albashi.