‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Matar Kansila a Abuja

Yan bindiga sun yi garkuwa da iyalan kansila mai wakiltar mazabar Gwako da ke Gwagwalada a Abuja.

Yan bindigar sun bukaci kudin fansar da ya kai naira miliyan 200 tun da fari sai dai sunyi ragi bayan tsananta roko.

Ba a samu sukunin jin ta bakin rundunar yan sanda ba dangane da faruwar al’amarin.

Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matan Idris Mohammed, kansila mai wakiltar mazabar Gwako da ke Gwagwalada, guda biyu hade da karin wasu mutane uku a birnin tarayya Abuja.

Ba a bayyane sunan matan kansilam su biyu ba, kanwar sa mace da kuma kannen sa maza su biyu ba har yanzu.

Wani makwabci, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya ce lamarin ya faru da misalin 12:08 na daren Litinin, lokacin da yan bindiga dauke da makamai suka yi wa gidan kansilan kawanya a kauyen.

Ya ce yan bindigar sun lalata babbar kofar shiga gidan bayan sun ragargaza ta da harsashi.

Daga nan, sai suka kutsa gidan suka kuma kwashe matan sa da kanwar sa da kuma kannen sa biyu lokacin barin wutar.

Ya ce kansilan, wanda yake dakin sa, ya sha da kyar ta wata kofar fita bayan ya gane cewa masu garkuwa da mutane ne suka kawo hari.

“Sai lokacin da ya fuskanci cewa maharan masu garkuwa da mutane ne, sai ya nemi tsira ta kofar baya. “Yanzu sun yi gaba da matan shi biyu, kanwar sa da kuma kannen maza da suke tare da shi,” a cewar sa.

Ya shaida cewa iyalan su sun sami sukunin tattaunawa da yan bindigar ranar Talata, kuma sun bukaci miliyan dari biyu kudin fansa.

“Amma maganar da nake yi yanzu sun rage kudin zuwa miliyan dari. Amma bayan tsananta roko sun dawo da kudin miliyan sha biyar,” in ji shi.

Ya kara da cewa daya daga cikin matan kansilan na da tsohon ciki.

Har yanzu ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja, ASP Maryam Yusuf ba, bata daga waya ko tayi martanin sakon da aka tura mata ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here