Birgediya Janar John Sure ya Shawarci Gwamnatin Tarayya Kan Tubabbun ‘Yan Boko Haram 

 

An nemi gwamnatin Najeriya ta gaggauta tura tubabbun ‘yan Boko Haram zuwa gonaki don yin noma.

Wannan shi ne matsayin Birgediya Janar John Sura (mai ritaya) wanda ya mayar da martani kan sabon ci gaba kan ‘yan ta’adda da suka tuba.

Ya ce ya kamata a dauke su a matsayin mutanen da ke zaman gidan yari sannan kuma a sanya su cikin yanayin da ke kasa da na ‘yan sansanin gudun hijira.

Tsohon shugaban horaswa da ayyuka a Hedikwatar rundunar Sojoji da ke Abuja, Birgediya Janar John Sura (mai ritaya), a ranar Juma’a, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tura ‘yan ta’addan Boko Haram sama da 1,000 da suka tuba zuwa gona.

A cewarsa, ya kamata a yi amfani da su wajen aikin gona da suka hana ‘yan gudun hijira da sauran ‘yan Najeriya yi.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken ‘Ku dauki ‘yan ta’addan Boko Haram da suka tuba a matsayin fursunonin yaki’, jaridar Punch ta ruwaito.

Sura, wanda ya bayyana ‘yan ta’addan da suka tuba a matsayin fursunonin yaki, ya bayar da hujjar cewa ya kamata a yi gyara ga Yarjejeniyar Geneva wacce ta ba su wasu gata kamar kariya daga duk wani aiki na tashin hankali gami da tsoratarwa, cin mutunci da sauransu.

Ya jaddada cewa ya kamata a kula da su a matsayin mutanen da ke zaman gidan yari kuma a sanya su cikin yanayin da ke ƙasa da na ‘yan sansanin gudun hijira.

Ya ce:

“Game da ‘yan Boko Haram da suka tuba, ya kamata a kula da su a matsayin mutanen da ke cikin kurkuku tare da aiki mai tsanani.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here