Gwamnatin Tarayya Zata Kara Zama Da Kungiyar ASUU Gobe

A ranar Juma’a Malaman Jami’a za su koma zama da Gwamnatin Tarayya.

Kungiyar ASUU ta shafe fiye da watanni takwas ta na yajin-aiki a Najeriya.

Zuwa gobe da safe za aji yadda tattaunawar ASUU da Gwamnati za ta kaya Jaridar This Day ta fitar da rahoto cewa wata babbar tawaga ta gwamnatin tarayya za ta gana da shugabannin kungiyar malaman jami’a, ASUU.

Bangaren gwamnatin tarayya za su yi zama da kungiyar ASUU ne a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, 2020, da nufin ganin karshen yajin-aiki.

Mataimakin darektan yada labarai na ma’aikatar kwadago, Charles Akpan, ya bada sanarwar wannan zama da gwamnati za ta yi da malaman jami’a.

Ministan kwadago, Ngige ya nuna cewa abin da za su iya ba ASUU ba zai zarce Naira biliyan 40 ba, sai kuma Naira biliyan 20 na gyaran jami’o’in kasar.

A halin yanzu kungiyar ta fara koka wa game da yadda tattaunawarsu da gwamnati ya ke daukar lokaci, malaman sun zargi gwamnati da yaudarar jama’a.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here