Za ka Ciza dan Yatsa Akan APC – PDP Zuwa Gwamnan Ebonyi

Gwamna Umahi na jihar Ebonyi na son kujerar takarar shugabancin kasa a zaben 2023 in ji PDP.

APC zata bashi kunya shi bai sani ba, a cewar wani jigon a jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Umahi ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar PDP sakamakon rashin adalci da ake yi wa yan yankin kudu maso gabas.

Jam’iyyar PDP ta ce jam’iyya mai mulki ta APC zata bawa gwamna Dave Umahi na Ebonyi a babban zabe mai gabatowa na 2023.

Umahi ya bayyana ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata, a zangon mulkin sa na biyu bayan an zabe shi karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Akwai yiwuwar Umahi na son takarar shugabancin kasa a zaben 2023, kuma yana neman jam’iyyar da zata bawa dan yankinsa takara ko zai samu gurbin tsayawa.

Sai dai ya karyata wannan batu a lokacin da ya yake bayani bayan komawarsa jam’iyyar APC, yake cewa, “na dawo wannan jam’iyya ne sakamakon irin rashin adalcin da ake wa yan yankin kudu maso gabas a PDP tun daga 1999 har yanzu.”

Da yake jawabi a taron shugabannin PDP karo na 90 da ya gudana a hedikwatar jam’iyyar PDP a Abuja, shugaban kwamitin amintattu, Sanata Walid Jibrin ya ce, “ina tausaya masa.”

“APC zata bashi kunya shi bai sani ba,” a cewar sa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here