Gwamnatin Tarayya Ta karbo Bashin Naira Biliyan daya Karkashin Ma’aikatar Kasuwanci

Gwamnatin Najeriya ta karbo bashin makudan kudade don tallafawa kananan masana’antu

Gwamnatin ta bayyana hakan a matsayin kokarin farfado da tattalin arzikin kasar da ya suma

An karbo bashin ne karkashin ma’aikatar kasuwanci, masana’antu da zuba hannun jari ta kasar

A kokarin farfado da tattalin arzikin kasa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya ta karbo bashin naira biliyan daya domin taimakawa masu kananan masana’antu, BBC ta ruwaito.

An karbo bashin ne ta hannun bankin masana’antu karkashin Ma’aikatar kasuwanci masana’antu da zuba hannayen jari ta kasar.

Adeniyi Adebayo na ma’aikatar ne ya bayyana hakan yayin wani shiri na karfafawa kananan masana’antu da aka yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here