‘Yan Banga a Jahar Ondo Sun kama Shanu Sama da 300

A karo na biyu, ‘yan bangan Amotekun sun sake kame wasu shanu da suka haura 300 a Ondo

A baya an kame shanu sama da 100 a kan hanyar Akure zuwa Ilesha ranar Lahadi da ta gabata

Wannan kame na shanu ya biyo bayan umarnin hana kiwo a fili da gwamnatin jahar ta sanya

Hanyar Oyemekun-Oba Adesida har zuwa Alagbaka ta cika da cunkoson ababen hawa a safiyar ranar Talata yayin da jami’an tsaron Amotekun a jahar Ondo suka kai shanu 300 da aka kama zuwa hedkwatarsu.

An kame shanu sama da 100 a ranar Lahadin da ta gabata a kan babbar hanyar Akure zuwa Ilesha saboda sabawa umarnin da gwamnatin jahar ta bayar kan hana kiwo a fili da kuma kiwon makiyaya masu karancin shekaru.

Lokacin da aka tuntube shi, Kwamandan Amotekun na jahar Ondo, Cif Adetunji Adeleye, ya ce yana wurin da ake gudanar da aiki amma ya yi alkawarin zai kira daga baya.

Har yanzu bai kira zuwa lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here