Gwamnatin Tarayya ta Assasa Karin Kasafi Don Cike Gibi a Shirin Farfaɗo da Sashen da Rikice-Riciken da ke Afkuwa

Ministan kula da Al’amuran jin kai da sarrafa annoba da cigaban Al’umma, Sadiya Umar Farouq ta kaddamar da aikin farfado da yau a garin Abuja.

Shirin na (MCRP) a karkashin Hukumar Raya Arewa maso Gabas yana neman karin kuɗaɗe don ci gaba da tallafawa jihohin BAY (Borno, Adamawa da Yobe) ta hanyar bayar da agaji da kuma farfado da tattalin arzikin na dogon lokaci da nufin tallafawa Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Jihohin Arewa maso Gabas don samun gyara da inganta muhimman ababen more rayuwa da kuma isar da ingantaccen aiki na bunkasa rayuwa.

Yayin kaddamar da aikin, ministan ta bayyana farin cikin ta da sakamakon da hukumar (MCRP) ta samu, tare da yabawa kungiyoyin dake gudanar da aikin bisa kwazon da suka nuna tun lokacin da aka fara aikin.

“Za mu ci gaba da ba ku kwarin guiwa da ku kara himma, duk da cewa mun samu gagarumar nasara wajen farfado da ci gaban yankunan, akwai sauran ayyuka da dama da za’a yi.

Wannan ya bayyana a cikin sabbin tsare-tsare na lambobin masu cin gajiyar shirin a cikin karin kudade na aikin da kuma shawarar da gwamnatin Najeriya da bankin duniya suka dauka na kara kudaden da kuma kara tsawon lokacin aikin.

Ƙarin kuɗaɗen aikin farfado da wasu sashe masu dimbin yawa wanɗan da rikice rikice ke yawan afkuwa, ya ba mu wata dama don ƙara ƙarfafa ci gaban da muka samu, tare da yin ƙarin aiki don tabbatar da cewa ’yan ƙasar da ke mabukata a faɗin jihohi ukun da aikin ya shafa za su iya dawo da rayuwarsu, samun ingantaccen kiwon lafiya. , ilimi, ruwa, tsaftar muhalli, tsafta da inganta hulda da zababbun jami’ai.

Aikin yana nufin sauƙaƙe Ingantattun ayyuka ba kawai ta hanyar gina ingantattun ababen more rayuwa ba face tabbatar da haɓaka ingancin ayyukan da aka aiwatar wa.

“Tare da habaka assasa ƙarin kudin shiga kamar yadda aka gabatar a baya, fifikon inganta darajar aikin gona ya taka muhimmiyar rawa a cikin dabarun ciyar da yankin gaba bisa tafarkin ci gaba mai dorewa.

Mun yi niyya a matsayinmu na gwamnati don samar da yanayin da jama’a za su amfana da dimbin filayen noma da ake amfani dasu ba don iya ciyar da kansu ba face har da ma jihohin da ke makwabtaka dasu”.

“Shigo da Najeriya a cikin ayyukan yankin na kasashen tafkin Chadi, wanɗanda ke makwabtaka damu; Kamaru, Nijar da Chadi, suna nuna mahimmancin musayar bayanai, tattaunawa akai-akai yayin da matsalolin sauyin yanayi, rashin aikin yi da rikice-rikice daban-daban suka mamaye iyakokinmu. Mafitar matsalolin da aka samo tare da kasashen dake da iyaka da Najeriya, za su ba da babbar dama don tasiri mai dorewa ga ƙasashenmu amma ga yankin tafkin Chadi.

Za mu yi aiki kafada da kafada da kasashen dake makwabtaka damu domin nemo mafita mai dorewa kan ƙalubalen da muke fuskanta tare”.

Sauran wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron sun hada da manajan darakta na hukumar raya yankin arewa maso gabas Mohammed G. Alkali, wakilan bankin duniya, kungiyar tarayyar turai, USAID da Ofishin Harkokin Waje, (Foreign Commonwealth and Development Office) FCDO.

Saleh Farouq Gagarawa

Mai Taimakon Media na waje

22-02-2022

Donmin

NNEKA IKEM ANIBEZE

SA MEDIA

22-02-2022

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here