Kudaden da Gwamnatin Tarayya ta Kashe Kan Cutar Korona – Musa Bello

 

Mutane 68 suka kamu da cutar Coronavirus a ranar Talata kadai a birnin tarayya.

Ministan Abuja ya bayyana iri taimakon kayan tallafin da suka yiwa mutanen birnin.

Har yanzu ana samun daruruwan yan Najeriya masu kamuwa da Korona kulli yaumin.

Ministan birnin tarayya Abuja, Muhammadu Musa Bello, ya bayyanawa majalisar dattawan tarayya cewa ya kashe kimanin bilyan 29 domin dakile cutar Korona a Abuja.

Yayin jawabi ga mambobin kwamitin birnin tarayya na majalisar dattawa, Ministan yace an kashe kudaden ne wajen inganta tsaro, kayan abincin rage radadin Korona, da kuma jihohin dake makwabtaka mabukata.

Ya kara da cewa gwamnatin Abuja ta taimakawa mazauna birnin da makwabta da kayayyakin kiwon lafiya.

A cewarsa, an yi amfani da yawancin kudin ne wajen samar da kayan abinci ga jama’a, saboda babu wanda ya kawo taimako lokacin da cutar Korona tayi tsauri.

Saboda haka ya bukaci yan majalisan su sake duba kasafin kudin birnin tarayya saboda yawan abubuwan da ke kasa.

Ya ce dubi cikin kasafin kudin da yake bukata wajen yan majalisa shine ta amince da abubuwa masu muhimmanci duk da cutar.

Shugaban kwamitin, Sanata Abubakar Kyari, ya jinjinawa birnin tarayya bisa yadda ta dakile cutar Korona.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here