Kasafin 2022: Gwamnatin Tarayya na Neman Bashin N4.89trn – Ministar Kudi
Gwamnatin tarayya tana neman bashin cikin gida da waje na naira tiriliyan 4.89 don cikasa kasafin kudin shekarar 2022 na naira tiriliyan 5.62.
Ministar ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed ce ta gabatar da wannan kudirin ga ‘yan majalisar wakilai a ranar Litinin.
A cewarta bisa tsarin kasafin shekara mai zuwa, gwamnatin tarayya zata rage yawan kudaden da take narka wa ma’aikatu, sasanni da hukumomi da naira biliyan 259.31.
Read Also:
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirinta na amso rancen cikin gida da na waje na naira tiriliyan 4.89 don samar da kudaden kasafin shekarar 2022 na naira tiriliyan 5.62.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Ministar kudi ta bayyana wannan kudirin a wata takarda da ta mika ga ma’aikatarta ne ga majalisar wakilai ta MTEF da FSP na 2022 zuwa 2024 a ranar Litinin.
Ministar ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, a gabatarwar da tayi ta ce gwamnatin tarayya za ta rage yawan kudaden da take narkawa ma’aikatu, sasanni da hukumomi da naira biliyan 259.31.
Ta bayyana yadda gibin da za a isa dashi 2022 na naira tiriliyan 5.62 ya karu fiye da naira tiriliyan 5.60 a 2021, Daily Trust ta ruwaito.