Gwamnatin Tarayya ba Hukuma Bace da za a Rika Daukan ko Wane Irin Mutane Aiki Domin Magance Matsalar Rashin Ayyuka a Kasar – Folashade Yemi-Esan

 

Gwamnatin tarayya ta nuna alamar tana shirin korar ma’aikata da ba su san makamashin aiki ba.

Folashade Yemi-Esan, shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ce ta sanar da hakan ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu.

Shugaban ma’aikata ta kasa ta ce wadanda suka cancanta ne kawai za a dauka aiki a hukumomin gwamnatin tarayya.

Folashade Yemi-Esan, shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, HoS, ta ce za a bullo da tsarin da zai tabbatar wadanda suka dace ne kawai za su samu aikin gwamnatin tarayya.

Vanguard ta ruwaito cewa Yemi-Esan ta yi wannan furucin ne a wurin taron Hukumar Yin Sauye-Sauye a ayyukan gwamnati, BPSR, da aka yi a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu a Abuja.

a ce akwai bukatar a yi waje da wadanda ba su san makamashin aiki ba. Emmanuel Meribole, Sakataren dindindin na bangaren tsare-tsare a ofishin na HoS ne ya wakilci Yemi-Esan a wurin taron.

A cewarta, a halin yanzu gwamnatin tarayya ba hukuma bace da za a rika daukan ko wane irin mutane aiki domin magance matsalar rashin ayyuka a kasar.

HoS din ta ce aikin gwamnatin tarayya na kan tsari ne na magance matsalar tattalin arziki, zamantakewa da muhalli na SDGs. Shugaban BPSR, Dasuki Arabi ya ce bayan annobar COVID-19, ana bukatar aiwatar da sabon tsarin aikin gwamnati na zamani da gwamnatin tarayya ta tsara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here