Gwamna Zulum ya Fadi Dalilin da Yasa Borno ta fi Abuja Tsaro a Yanzu

 

Gwamna Babagana Zulum na jahar Borno ya ce a halin yanzu Borno ta fi Abuja tsaro.

Zulum ya ce jahar ta cimma wannan nasarar ne ta hanyar amfani da ‘yan sintiri wurin samar da tsaro .

Zulum ya ce tuni har yan sintirin sunyi nasarar fatattakan ‘yan ta’adda sun koma dajin Sambisa.

Gwamnan jahar Borno, Babagana Zulum, a ranar Juma’a ya ce yana amfani da yan sintiri/ ‘yan sakai wurin magance kallubalen tsaro da jaharsa ke fama da su, Vanguard ta ruwaito.

Zulum ya yi furta hakan na a Owerri, a lokacin da ya karbi wasikar gayyata domin bashi lambar yabo na shugabanci da kungiyar yan jaridar Nigeria, NUJ, reshen jahar Imo ta aika masa.

Emma Odibo, sakataren NUJ na jahar Imo ne ya gabatar da wasikar a madadin shugaban kungiyar Chris Akaraonye.

Zulum wanda ya samu wakilcin babban mai taimaka masa na musamman a bangaren watsa labarai, Baba Shaikeh Haruna, ya ce yan sakai na cikin matakan da gwamnatin Zulum ta dauka domin kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.

A cewar Zulum:

“Mu a Borno sun shafe shekaru 12 muna fama da kallubalen tsaro, sai dai abubuwa da yawa sun canja cikin matakan da muka dauka shine amfani da yan sintiri domin samar da tsaro a jahar; su ke samar da tsaro a jahar har sun fatattaki yan ta’adda zuwa dajin Sambisa.

“Idan ka zo Maiduguri, za ka yi mamaki, har ya fi Abuja tsaro. Wasu lokutan yadda mutane ke magana kan batun tsaro a Borno, ba haka za ka gan shi ba idan ka zo jahar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here