Sanata Ali Ndume ya Bukaci Gwamnati da ta Kara Kasafin Kudin Makamai Don Magance Matsalar Tsaro

 

Shugaban kwamitin majalisa na kula da rundunar sojin Najeriya, Sanata Ali Ndume yace akwai bukatar kara kasafin kudin makamai.

Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta kudu, yace Najeriya bata mayar da hankali ba wurin yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram.

Ndume yace idan misali gobara ta tashi a gidan mutum, ai ba tsayawa zai yi auna wutar kashe gobarar ba, zuba ruwa ake har ta mutu.

Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazabar Borno ta kudu, yace kasafin kudi N29 biliyan da aka yi domin manyan ayyukan sojoji a 2021 ya nuna yadda Najeriya bata mayar da hankali ba wurin shawo kan matsalar tsaro.

A yayin hira da gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis, Ndume ya tabbatar da cewa kasashe kamarsu Chadi da Kamaru na kashe kudade masu yawa fiye da yadda Najeriya ke yi a fannin tsaro

Ana ta kiran gwamnati da ta inganta kasafin sojin Najeriya bayan tsanantar hare-hare da ‘yan ta’addan Boko Haram ke yi a yankin arewa maso gabas.

A cikin kwanakin nan ne Ibrahim Attahiru, shugaban sojin kasan Najeriya ya bukaci majalisar dattawa da ta kara kasafi ga rundunar domin siyan makamai.

Kamar yadda Ndume wanda shine shugaban kwamitin kula da rundunar soji a majalisar dattawa, yace Najeriya na fuskantar matsananciyar damuwa da ‘yan ta’addan Boko Haram kuma hakan yasa dole a fifita fitar da kudade domin rundunar sojin.

“Idan gidanka gobara ta tashi, zaka auna ruwan da zaka kashe gobarar ne da shi? Muna cikin matsala, ballantana a yankin arewa maso gabas,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here