Mutane su Kare Kan su Daga ‘Yan Bindiga: Gwamnatin Tarayya ta yi Magana Kan Batun Gwamna Masari

 

Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta ce bata goyon bayan kiran da Masari ya yi na cewa mutane su tashi su kare kansu daga ‘yan bindiga.

Gwamnatin ta bakin Ministan Harkokin Yan sanda, Mohammed Dingyadi ya ce Masari na da ikon ya bayyana ra’ayinsa.

Dingyadi ya ce gwamnatin tarayya ba ta goyon bayan mutane su dauki makamai ba bisa ka’ida ba sai dai samar da yan sandan unguwa.

FCT Abuja – Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kiran da Gwamna Aminu Masari na jahar Katsina da takwararsa na Jahar Benue, Samuel Ortom, da wasu kungiyoyi da mutane suka yi na cewa mutane su kare kansu daga ‘yan bindiga, rahoton Daily Trust.

Ministan Harkokin ‘Yan sanda, Mohammed Dingyadi, yayin jawabin shekara-shekara na ma’aikatarsa karo na biyu a hedkwatar ‘yan sanda a Abuja ya ce gwamnati bata goyon bayan mutane su dauki makamai da kansu.

Sannan, Ministan ya kara da cewa Masari yana da ikon fadin ra’ayinsa kamar yadda rahoton Daily Trust ya bayyana.

A cewar Dingyadi:

“Ya kamata mu sani cewa a Nigeria muke, inda kowa ke da ikon fadin ra’ayinsa. Ina tunanin gwamnan na da damar neman yin abin da ya ke ganin ya dace a jaharsa.”

Amma, ya ce hakan na kan tsari idan har za a kare kai ne ta hanyar samar da ‘yan sandan unguwanni don inganta tsaro.

Dingyadi, ya kuma ce kallubalen da jami’an tsaro ke fuskanta shine yakin sunkoro da yan bindigan ke yi na hari sannan su gudu amma sojojin za su magance matsalar.

A cewarsa, gwamnati da hukumomin tsaro na bukatar hadin kan al’ummar kasa da goyon baya don ‘gwamnatin za ta iya magance matsalar.’

Ya cigaba da cewa ba a tsammanin mutane su kwanta ba tare da daukan matakan kare kansu ba, su kare makwabtansu da unguwanninsu, wannan shine manufar samar da yan sandan unguwanni.

“Kowa ya bada gudunmawarsa wurin yaki da laifuka. Abin da muke cewa shine kada mutane su dauki makamai ba bisa ka’ida ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here