2023: Ifeanyi Okowa Tare da Gwamnoni 5 da Ka Iya Zama Sanatoci

 

Shekarar 2021 muke amma batun zaɓen 2023 ya karaɗe ko ina a Najeriya.

A 2023, da yawa daga cikin gwamnonin Najeriya na kammala wa’adin mulkinsu karo na biyu.

Tuni dai wasu gwamnonin Najeriya suka fara tattara komatsansu don komawa majalisar dattawa A yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa, wasu daga cikin gwamnonin Najeriya suna kammala wa’adin mulkinsu karo na biyu kuma suna ƙokarin takarar kujerar majalisar dattawa a jahohinsu.

Komawar gwamnoni majalisa ta zama al’ada a siyasar Najeriya saboda suna kallon majalisar dattawa a matsayin wurin komawa bayan murabus.

Ga wasu, samun kujera a majlisar yana sa a cigaba da damawa dasu a siyasa.

1. Ifeanyi Okowa

Okowa likita ne wanda ya koma siyasa. Yana ɗaya daga cikin taurarin dake haske a PDP. Ɗan siyasa ne nagari kuma akwai yuwuwar ya koma majalisar dattawa a karo na biyu domin ya kasance ɗan majalisa a majalisar dattawa karo na 7.

2. Ifeanyi Ugwuanyi

Gwamnan jahar Enugu ba sabo bane a siyasar majalisa saboda tsohon ɗan majalisar wakilai ne.Saboda ƙokarinsa ne zai sa jama’arsa su zaɓe shi domin zama a majalisar dattawa.

3. Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jahar Kano zai kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu a 2023. Mamallakin digirin digirgir din yayi aiki sosai a fannin ababen more rayuwa a jahar Kano. Akwai yuwuwar gwamnan ya nemi matsuguni a majalisar tarayya.

4. Abubakar Sani Bello

Akwai yuwuwar gwamnan jahar Neja ya koma majalisa a 2023. A bangaren Bello, har yanzu da ƙuruciyarsa kuma yana da biyayya ga magabata masu faɗi a ji a siyasar yankin.

5. Okezie Ikpeazu Jahar Abia bata taɓa sa’ar da tayi ba na shugaba kamar daga 2015 kuma ta fara ganin sauyi a lamarin mulki. Akwai yuwuwar gwamnan ya koma majalisar dattaaa domin cigaba da ayyukan alherinsa.

6. Udom Emmanuel Gwamna Udom Emmanuel na jahar Akwa Ibom yana ɗaya daga cikin gwamnonin da za su ƙare a majalisar dattawa a matsayin sanata a 2023.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here