Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 11 a Jahar Abia

Mutune 11 sun mutu sakamakon artabu tsakanin sojoji da yan bindiga a garin Abia.

Yan bindigan ne suka afkawa sojojin a Ariaria a Abia yayin da suka fito sintiri bayan samun rahotannin sirri.

Wasu majoyoyin sun ce a kalla mutum 16 ne suka rasu amma rundunar soji ta ce mutum 11 ne kuma babu soja da ya mutu Mutane sun shiga firgici a birnin Aba, cibiyar kasuwanci na jahar Abia a yayin da a kalla mutane 11 suka mutu sakamakon musayar wuta da yan bindiga suka yi da sojoji a daren ranar Talata, Vangaurd ta ruwaito.

An kai wa sojojin hari a shingen da suka kafa ne kwanaki biyu bayan wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kashe yan sanda uku a Abariba, karamar hukumar Ohafia na jahar.

Yan bindigan da aka ce sun kai 50 sun afka wa mutanen da ke shataletalen Ariaria a babban titin Enugu/Port harcourt misalin karfe 8.30 na daren ranar Talata suka kai wa sojojin hari.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa kafin yan bindigan su iso, sojojin sun fito sintiri ne sakamakon bayannan sirri da suka samu.

Yayin da wasu rahotanni sun ce mutane 16 aka kashe, cikinsu biyu sojoji, majiya daga rundunar sojoji ta ce mutane 11 ne suka mutu kuma babu soja a cikinsu.

Wani mazaunin unguwar wanda ke kan hanyarsu zuwa coci a daren ya shaidawa wakilcin majiyar Legit.ng cewa dole ya fasa zuwa inda zai tafi sakamakon musayar wutar da sojojin da yan bindigan suka yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here