VAT Maimakon FIRS: Gwamnonin Najeriya 9 da Suka Dage Sai Jahohi Sun Karbi Harajin

 

Gwamnonin kudu sun yi wani taro a Enugu don tattauna muhimman batutuwa da yankin ke fuskanta.

Daya daga cikin mahimman batutuwan da suka tattauna shine na karbar harajin VAT.

Yayinda wasu jahohi ke adawa da FIRS kan karbar haraji wasu na goyon bayan gwamnatin tarayya.

Najeriya – A ranar Alhamis, 16 ga Satumba, gwamnoni a Kudancin Najeriya sun yi wani taro a Enugu don tattauna muhimman batutuwa da yankin ke fuskanta.

Daya daga cikin mahimman batutuwan da suka tattauna shine na karbar harajin VAT.

Hukumar tattara kudaden shiga ta tarayya (FIRS) ce ta saba karbar harajin VAT har zuwa kwanan nan da gwamnatin jahar Ribas ta kalubalanci hukumar ta tarayya.

Gwamnatin jahar Legas ta bi sahu yayin da gwamnoni ke neman kwace ikon karbar harajin VAT daga gwamnatin tarayya.

Yanzu haka lamarin yana kotun daukaka kara bayan da gwamnatin jahar Ribas ta yi nasara a matakin babbar kotun tarayya.

Yayin da gwamnoni da yawa ke goyan bayan jahohi su rika karbar harajin VAT, akwai kuma wasu kalilan da ke ganin ya kamata FIRS ta ci gaba da karbar harajin.

A taron gwamnonin kudancin kasar, rahotannin kafafen yada labarai sun bayyana cewa sun hadu sun goyi bayan karbar VAT daga jahohi.

Sai dai kuma, Legit.ng ta lura cewa wasu gwamnoni ba su halarci taron ba, sun zabi tura mataimakan su.

Idan aka yi la’akari da wannan yunƙurin, yana da wahala a iya tantance idan da gaske duk gwamnonin kudancin ƙasar suna goyon bayan jahohi su harajin VAT.

Hakanan yana da mahimmanci a lura cewa daya daga cikin gwamnonin kudancin, David Umahi na Ebonyi, a baya ya goyi bayan FIRS don ci gaba da tattara VAT.

Ga jerin gwamnonin da suka goyi bayan jahohi su karbi harajin VAT, maimakon FIRS:

1. Oluwarotimí Akeredólu (SAN) – gwamnan jahar Ondo

2. Ifeanyi Ugwuanyi – gwamnan Enugu

3. Nyesom Wike – gwamnan jahar Rivers

4. Emmanuel Udom – jahar Akwa Ibom

5. Babajide Sanwo -Olu – jahar Legas

6. Ifeanyi Okowa na Delta – jahar Delta

7. Adegboyega Oyetola – jahar Osun

8. Douye Diri – jahar Bayelsa

9. Dapo Abiodun – Jahar Ogun

Kamar yadda jaridar The Sun ta rawaito, gwamnoni tara ne suka hallara yayin da bakwai suka tura mataimakan su daga cikin jahohi 17 na yankin.

Gwamnan jahar Anambra, Willie Obiano, ba ya nan kuma bai aiko da wani wakili ba.

Gwamnoni da ba sa goyon bayan jahohi su karbi VAT

Yahaya Bello

Kamar dai Ebonyi, gwamnatin jahar Kogi ta ce ba za ta saka kanta a cikin shirin karbar VAT ba kamar yadda gwamnatocin Legas da Ribas suka fara ba.

Yunkurin da jahohin biyu suka yi ya samu adawa daga jahar Kogi ta hannun kwamishinan yada labarai, Kingsley Fanwo, inji rahoton The Punch.

Muhammad Inuwa Yahaya

Haka kuma, gwamnatin jahar Gombe tana adawa da karbar harajin VAT da jahohi ke son yi.

Jaridar The Punch ta rawaito cewa kwamishinan kudi da raya tattalin arzikin jahar, Muhammad Magaji, ya roki Legas da Ribas da su kasance masu tsaron ‘yan uwansu ta hanyar bayar da gudunmawa ga cibiyar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here