Farfesa Gwarzo Zai Gabatar da Mukala a kasar Togo
Shugaban rukuni jami’oin Maryam Abacha(MAAUN) da Franco British international(FBIU) Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, zai gabatar da mukala a kasar Togo a yayi daukar dalibai a jami’ar IHERIS a karon na takwas.
Farfesa Gwarzo wanda shine shugaban Kungiyar jami’oi masu zaman Kan su na afrika (AAPU), na cikin Jeri manyan Baki da aka gayyato a fadin duniya ta fannin inganta hakar ilimi da Kuma taimakawa al’umma a bangarorin ci gaban Mai dorewa.
Read Also:
Mukala da farfesa Gwarzo zai Gabatar zatayi duba ne akan muhimmaci hadin Kan jami’oi masu zaman kansu a nahiyar Afrikan tare da kawo sauyi Mai muhimmaci wajen tafiyantar da salon kawo cigaba a jami’oi masu zaman kansu a nahiyar afrika ta fanni bincike,talllawafawa sababin fannonin na kimiya da fasaha , karfafa a’laka a tsakanin shuwagabanin jami’oi.
Taron Kara wa juna sanin na salle De da farfesa Adamu Abubakar Gwarzo zai hallarta a ranar 30 ga wata oktoba a cikin shekara 2021 a Eda -oba lome, a kasar Togo.
shugaban rukuni jami’oi Maryam Abacha (MAAUN) da Franco British international (FBIU) Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, yayi Shura a idon duniya ta fanni kawo cigaban ilimi da Kuma tallafawa mabukata a nahiyar afrika .