Yadda Hadimin Atiku ya Caccaki Tinubu
Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Phrank Shaibu ya bayyana Bola Tinubu a matsayin wanda bai cancaci zama shugaban kasa ba.
Shaibu ya bayyana hakan ne bayan wata kwabsawa da Tinubu ya yi a wani taron da aka gudanar a jihar Kaduna.
Dan takarar shugaban kasa na APC ya yi tsokaci game da ayyukan gwamna Nasir El-Rufai, ya ce ya ‘sauya rubabbun lamurra zuwa munana’.
FCT, Abuja – Jigon jam’iyyar PDP Phrank Shaibu ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
A wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng a jiya Lahadi 16 ga watan Oktoba, Shaibu ya bayyana cewa, duba da lafiyar Tinubu, bai cancanci ya gaji shugaban kasa Buhari ba.
Ya kuma bayyana cewa, Tinubu ya sha kwabsawa a maganganunsa tun bayan da ayyana aniyarsa ta zama shugaban kasa, wanda hakan ke nuna a rude yake gaba daya.
Tinubu a rude yake, kuma bai da lafiya, inji hadimin Atiku
Shaibu, wanda kuma shine mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce maganar Tinubu ta baya-bayan nan a Kaduna ta sake nuna rudewar Tinubu.
Ya bayyana cewa:
“Tinubu ya gaji, ya kamata ya tafi gida ya huta.
Read Also:
“Idan kuka kalli dan takarar shugaban kasan APC, za ku ga mutumin da ya gaji kuma mai rauni. Kuma kun sha jin irin kwabsin da ya sha fitowa daga gare shi tun ma kafin ya fara gangamin kamfen.”
Najeriya na bukatar mai jini a jika, bayanin Phrank
Ya kara da cewa:
“Najeriya a yanzu na cikin wani irin mawucin yanayi da a kowane fanni na tattalin arziki na cikin cakwalkwali; don haka, kasar nan ba zai yiwu ta koma karkashin shugaban kasa mara lafiya ba.”
Ya kuma tunawa ‘yan Najeriya cewa, a ranar Labara, 8 ga watan Yuni, kadan ya hana Tinubu ya fadi a lokacin da yake magana a Eagle Sqaure, inda aka yi taron gangamin APC.
Ya kuma bayyana cewa, yayin da Tinubu ke magana a taron gangamin, an ga hannayensa na rawa, lamarin dake nuna akwai alamar tambaya ga lafiyarsa.
Atiku ya kamata a zaba, inji jigon APC
Ya kara da cewa:
“Kasar nan na bukatar shugaban da ya cancanta. Ofishin shugaban kasa ba na mutum mara lafiya bane. Tinubu yi iyakar kokarinsa amma dai yanzu ya gaji kuma ya kamata ya koma gida domin ya cancanci ya huta.”
Hakazalika, ya bayyana damuwar cewa, a nahiyar Afrika ne kawai ake samun mara lafiya amma ya dage sai ya dale kujerar shugabanci, duk kuwa irin matsalar tattalin arzikin da kasa ke fuskanta.
Daga karshe ya shawarci masu kada kuri’u da su zabi Atiku, tare da cewa, shi kadi ne zai iya daidaita kasar nan.