Mutane 11 Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Hatsarin Mota a Hanyar Bauchi

 

Akalla mutum 11 ne suka mutu wasu tara kuma suka ji raunuka sakamakon wani hatsarin mota da ya auku ranar Asabar a daidai kauyen Hawan Jaki da ke Alkaleri a kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.

Jaridar The Nation a Najeriya ta ruwaito cewa hadarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, inda hadarin ya rutsa da wata motar bas da kuma babban motar dakon kaya wadanda suka yi taho mu gama.

Babban kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kaa rashen Bauchi, Yusuf Abdullahi, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya tabbatar da cewa wasu mutum 10 kuma sun jikkata.

Abdullahi ya dora laifi yawan hadura da ake samu kan tukin ganganci, inda ya kara da cewa mutum tara sun mutu nan take yayin da sauran biyun kuma suka rasu a asibiti.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here