ALLAH ya yi wa Matar Tsohon Shugaban Kasa, Hadiza Shehu Shagari Rasuwa

 

Matar marigayi tsohon Shugaban kasa, Hadiza Shehu Shagari ta amsa kiran Allah.

Hajiya Hadiza ta rasu a yau Alhamis, 12 ga watan Agusta bayan ta yi fama da cutar corona.

Za a yi jana’izarta bayan sallar La’asar a babban masallacin kasa da ke Abuja Allah ya yi wa Hadiza Shagari, matar marigayi tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari rasuwa, tana da shekaru 80 a duniya, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Wata sanarwa da ‘dan tsohon shugaban kasar, Bala Shagari ya fitar, ya bayyana cewa ta mutu ne sakamakon cutar korona a cibiyar killace masu cutar da ke Gwagwalada.

Ya kuma bayyana cewa za a yi jana’izarta a yau Alhamis, 12 ga watan Agusta, bayan sallar la’asar a babban masallacin kasa da ke Abuja, Solacebase ta ruwaito.

Sanarwar ta zo kamar haka:

“Mun rasa ta da sanyin safiyar yau, 12 ga watan Agusta 2021, da misalin karfe 3:00am, bayan ta yi fama da Covid-19 a Cibiyar Killace masu ita na Gwagwalada da ke Abuja.

“Hajiya Hadiza Shehu Shagari ta na da shekaru 80 a duniya. Za a yi Sallar Jana’izarta a yau, da karfe 4:00 na yamma bayan sallar la’asar, a Masallacin Kasa, Abuja.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here