Ana Haifar Jarirai 8,933 a Cikin Mako Daya a Saudiyya

 

Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta bayyana cewa jarirai 8,933 ne aka haifa cikin mako daya a kasar.

Ma’aikatar ta ce alkaluman sun kama daga ranar 23 ga watan Agusta zuwa 30 na wannan watan.

Birnin Riyadh ne sahun gaba na yawan jarirai da aka haifa, inda birnin ke da sabbin haihuwa 2,286, sai Makkah inda ake da jarirai 1,804, inda gabashin kasar ke da 868.

Alkaluman sun nuna cewa yankin Najran na da jarirai sabbin haihuwa 249, sai yankin Asir mai 586 da Hafr Al-Batin mai 205 da yankin Hail mai 192 da Jazan mai 466 sai kuma birnin Tabuk da ke 291 inda birnin Bisha kuma ke da jarirai sabbin haihuwa 124.

A birnin Madinah kuma na da sabbin haihuwa 636, yayin da ake da 511 a Qassim da kuma 104 birnin Al-Qurayat.

A yankin arewacin kasar kuma, jarirai 166 aka haifa yayin da a Al-Jouf kuma ake da 185 sai biranen Al-Baha da Al-Ahsa da ke da jarirai 109 da 351.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here