Hajji/Umara: Ana Ci gaba da Jan Hankalin Masu ɗauke-ɗauken Hoto a Harami

 

Shafin da ke wallafa bayanai kan masallatan harami na Makkah da Madina da ke ƙasar Saudiyya na ci gaba da shawartar masu ibada da su guje wa ɗauke-ɗauken hotun a lokacin da suka je domin yin ibada.

Shafin Haramain Sharifain ya wallafa a cikin harsuna da dama na duniya, ciki har da Hausa, cewar mutane su mayar da hankali wajen ibada tare da ƙaurace wa amfani da wayoyinsu, musamman wajen ɗaukar hotuna.

Saƙon ya ce: “Ya mai aikin Hajji mai daraja, da fatan za ka ajiye wayarka a gefe yayin da kake cikin ibada”.

Haka nan saƙon ya yi kira ga maza da su guje wa ɗaukan hotunan mata a cikin masallatan na harami.

“Don Allah kada ka ɗauki hotuna ko bidiyo na mata—hakan ya haramta,” kamar yadda saƙon ya bayyana.

Miliyoyin mutane yanzu haka suka yi tururuwa zuwa masallacin Ka’aba da ke birnin Makkah domin yin ibada da kuma masallacin annabi Muhammad da ke Madina domin ziyara.

Sai dai da alama yawan amfani da wayoyi wajen ɗaukan hoto ya zamo abin damuwa ga hukumomin gudanarwar masallatan, wanda hakan ne ya sanya suke ci gaba da faɗakarwa ga masu ibada da su ƙaurace wa irin hakan.

Ka’aba da kuma masallacin Madina na daga cikin wurare mafiya tsarki Musulmai, inda a kowace shekara miliyoyin mabiya addinin ki kai ziyara domin gudanar da aikin Hajji ko kuma Umara.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here