Hanga ya Karbi Shaidar Cin Zaɓen Sanatan Kano ta Tsakiya
Sanata Rufa’i Sani Hanga ya tabbatar wa BBC cewar Hukumar zaɓen Najeriya (INEC) ta damƙa masa shaidar cin zaben sanatan mazaɓar Kano ta tsakiya.
Read Also:
A jiya Talata ne INEC ta bai wa Rufa’i shaidar, bayan hukuncin Kotun Ƙolin Najeriya, da ta tabbatar da wanda kotun ɗaukaka ƙara ta yi inda ta umarci hukumar ta ba shi shaidar cin zaɓe duk da cewa babu sunansa a cikin jerin masu takarar sanata a mazaɓar ta Kano ta tsakiya, a zaben ranar 25 ga watan Fabarairun, 2023.
Da fari, INEC din ta bayyana Mallam Ibrahim Shekarau ne a matsayin wanda ya yi nasara a zaben karkashin jam’iyyar NNPP, duk da cewar ya koma jam’iyyar PDP.
Tun farko Mallam Ibrahim Shekarau ne ɗan takara, sai dai ya fice daga jam’iyyar ta NNPP daga baya tun kafin zaɓe, inda NNPP ta maye gurbinsa da Sanata Rufa’i Sani Hanga.
Amma hukumar zaɓen ta ce lokaci ya ƙure na sauya sunan Ibrahim Shekarau da na Rufa’i Sani Hanga.