Atiku da Jam’iyyarsa Sun Janye ƙarar Duba Kayan Zaɓe

Ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, wato Atiku Abubakar, shi da jam’iyyarsa sun janye sabuwar ƙarar da suka shigar ta neman tilasta wa hukumar zaɓe ba su damar duba kayan da aka yi amfani da su a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu.

Atikun da jam’iyyarsa da ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen da aka ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyya mai mulki APC a matsayin wanda ya ci zaɓen, sun shaida wa kotun musamman da ke sauraren ƙararraki kan zaɓen shugaban ƙasar a Abuja cewa ba su da buƙatar ci gaba da ƙarar.

Jagoran ayarin lauyoyin da ke wakiltar Atikun da PDP Mista Joe-Kyari Gadzama (SAN) shi ne ya shaida wa kotun haka lokacin da aka zauna fara sauraren ƙarar a yau Laraba.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa wani daga cikin lauyoyin na Atiku da PDP, wanda bai yarda a ambaci sunansa ba, ya ce tun da farko sun shigar da ƙarar ne saboda matsaloli da ƙalubalen da suka gamu da su lokacin da wakilan jam’iyyar da Atiku suka je hukumar zaɓen domin a ba su kayan su duba, kamar yadda kotu ta bayar da umarni.

Ya ce, to kasancewar kafin a zo sauraren wannan ƙara da suka shigar ta tilasta wa INEC barin wakilan su duba kayan zaɓen, INEC da kanta ta fito ta yi alƙawarin ba su damar su je su duba wasu daga cikin kayan musamman ma takardar da aka yi zaɓe, ya ce saboda haka ne suka janye wannan sabuwar ƙara.

Atiku da jam’iyyar tasa da kuma ɗan takarar Labour shi ma da jam’iyyar tasa dukkaninsu suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na Najeriya, inda kowanne daga cikin ɓangaororin biyu ke iƙirarin shi ne ya yi nasara aka yi masa fashi, tare da lasar takobin ƙwato nasarar tasu a kotu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here