Bamu da Hannu Cikin Dakatar da Sheikh Ibrahim Khalil – Kungiyar Malamai ta Jahar Kano
Wata kungiyar malamai ta jahar Kano ta yi watsi tare da nisanta kanta da dakatar da Sheikh Ibrahim Khalil.
 Kamar yadda takardar da ta samu sa hannun wasu manyan malaman Kano ta nuna, sun ce ba su da hannu cikin wannan hukuncin.
 Malaman sun sanar da cewa su masu assasa zaman lafiya da hadin kan Musulmi ne, don haka a kwantar da hankula a jahar.
Kano – Kasa da sa’o’i 24 bayan majalisar malamai ta Kano ta dakatar da Sheikh Ibrahim Khalil tare da maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, wata kungiyar malamai ta jahar Kano ta nisanta kanta daga wannan sanarwar.
 Daily Trust ta rawaito cewa, majalisar malaman ta ce ta dakatar da malamin ne kan zarginsa da siyasantar da lamurran majalisar.
Amma, a takardar da kungiyar ta sanar wacce sakataren ta, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa ya fitar, ta ce ba su da hannu a wannan hukuncin na dakatarwan.
Takardar ta kara da cewa, kungiyar ta kasance mai neman zaman lafiya tare da hadin kai tsakanin Musulmi a jahar, inda ta ja kunnen cewa wannan hukuncin na iya tabarbara wasu lamurra.
Ta kara da kira ga mazauna jahar Kano da su kwantar da hankulansu tare da yin watsi da duk wani lamari da zai iya kawo tashin-tashina, Daily Trust ta wallafa.
Sauran wadanda suka saka hannu kan takardar sun hada da fitattun malamai kamar su Farfesa Musa Muhammad Borodo, Sheikh Kariballah Sheikh Nasiru Kabara, Sheikha Abdulwahab Abdallah, Farfesa Mohammed Babangida Mohammad, Dr. Bashir Aliyu Umar, Imam Nasiru Mohammad Adam da Dr. Bashir Mu’azzam Mai Bushira.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here