Har da Hannun ‘Yan Siyasa a Rashin Tsaron Kasar Nan – Gwamna Ortom

 

Gwamnan jahar Benue ya bayyana cewa, akwai hannun ‘yan siyasa a rashin tsaron kasar nan.

Ya kuma bayyana yadda ‘yan siyasa suka shigo da sojojin kasashen waje don aikata barna a kasar.

Ya kuma ce, watsi da sojojin hayan ne ya jawo tabarbarewar tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu Gwamnan jahar Benue, Samuel Ortom, ya ce akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa wasu jami’an gwamnatin Najeriya na hada baki da masu satar mutane don aikata mummunan aikinsu, Arise Tv ta ruwaito.

Mista Ortom ya ce ‘yan siyasar da ke da wata manufa sun shigo da sojojin haya na kasashen waje don taimaka musu su ci zaben 2019.

Ya lura cewa watsi da wadannan sojojin haya shi ya haifar da tabarbarewar yanayin tsaro a kasar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da yake gabatar da lacca a Makon ‘Yan Jaridu na 2021 mai taken: “Rashin tsaro a Najeriya: Maido da Zaman Lafiya, Hadin kai da Ci gaba” kuma kungiyar Hadin kan ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya.

“Akwai wani kasuwancin da ke kawo riba a Najeriya tare da tsananin zaton hada kai da jami’an Gwamnati,” in ji gwamnan.

“Karuwar sace-sacen mutane a kowane bangare a fadin kasar lamari ne mai hatsari. Ba mu san wanda yake fadin gaskiya ba.

“Amma kamar yadda yake a yanzu, akwai zargi mai karfi da ke nuna cewa ‘yan siyasar da ke cikin wahala sun shigo da sojojin haya na kasashen waje don taimaka musu su ci zabe.

“Abin takaici, bayan da aka fadi zabe aka kuma ci nasara, aka yi watsi da sojojin hayan wadanda ke haifar da tabarbarewar tsaro a kasar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here