EU ta Haramta wa Ma’aikatanta Amfani da Manhajar TikTok
Hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai ta faɗa wa ma’aikanta da su cire manjahar TikTok mallakar ƙasar China daga wayoyinsu na aiki da sauran naurori saboda dalilan tsaro.
Read Also:
Mai magana da yawun hukumar Sonya Gospodinova ta ce EU ta ɗauki wannan matakin ne domin inganta tsaro a harkar intanet ɗin ta.
Gwamnatocin ƙasashen yamma na fargabar cewa China za ta iya amfani da manhajar mai farin jini domin leƙen asiri.
A bara ne gwamnatin Amurka ta hana amfani da Tik-Tok ɗin a naurorinta.
Sai dai kamfanin Tik-Tok ya ce akwai rashin fahimta a matakin da EU ta ɗauka.