Babu Wani Harin da ‘Yan Boko Haram Suka Kai Min – Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya musanta labaran kai masa hari da yayita yawo.

Kamar yadda hadiminsa na harkar yada labarai, Malam Isa Gusau ya rubuta a wata takarda.

Yace Zulum yaje Baga har ya kwana daya, wurin raba wa mutane 5000 kayan tallafi, kuma ya dawo lafiya.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya musanta labarin kai masa hari da ‘yan ta’adda suka kara kai wa tawagarsa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

“Ba a kai masa hari ba, balle tawagarsa,” kamar yadda Malam Isa Gusau, hadimin Zulum na harkar watsa labarai ya sanar a wata takarda.

A cewar Gusau, Zulum ya je Baga, inda yayi kwana daya yana kula da rabon kayan abinci da sauran kayan tallafi, sannan ya koma Maiduguri ba tare da wani abu ya same shi ba.

“Mun rubuta wannan takardar ne don mu sanar da cewa babu abinda ya samu Zulum ko kuma wani dan tawagarsa, muna musanta labarin da yake ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wanda yake nuna an kai wa gwamna Zulum farmaki.

“Tabbas gwamnan ya je Baga a ranar Asabar har washegari Lahadi yana garin, don ya kula da raba kayan abinci da kudin tallafi da aka bai wa mutane 5000 mazauna yankin. Ya samu damar duba gyare-gyare da kuma gine-ginen da gwamnati ta yi a wurin, ba tare da wani abu ya same shi ba.

“Muna son a tabbatar wa da mutane cewa ba gaskiya bane labarin da ake yadawa. Zulum da tawagarsa su na cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali,” Gusau yace.

“Kamar yadda kowa ya shaida, al’adar Farfesa Zulum ne fadin labarai yadda suke, kuma da a ce an kai masa farmaki, tabbas zai fadi.

Babu wani hari da aka kai masa ko tawagarsa, idan wani mai neman labari yana bukatar tabbatarwa, zai iya tuntubar sojojin Najeriya.

“Sannan gwamna Zulum yana mika sakon godiyarsa ga duk masu masa fatan alkhairi, sannan ya jinjina wa jami’an tsaro da ‘yan sa kai a kan kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno,” kamar yadda takardar tazo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here