Dalilin Ziyarar Shugabannin APC Zuwa Villa

Gumurzun siyasa tsakanin dattijon jam’iyyar PDP, Bode George, da abokin karawarsa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu,ya sake ɗaukar zafi.

George ya sake kunno wutar rikicin ne bayan ya yi iƙirarin cewar ziyarar da jiga-jigan dattijan jam’iyyar APC suka kai Villa sun yi ne a madadin Tinubu.

Duk da Tinubu bai maida martanin bisa iƙirarin ba, ɗaya daga cikin shugabannin APC ya yi watsi da iƙirarin nasa Chief Bode George, babban jigo a jam’iyyar PDP a kudu maso yamma, ya maida martani a kan ziyarar da shugabannin jam’iyyar APC suka kaiwa shugaban ƙasa a fadarsa ta Aso rock ranar Juma’a.

Tsofaffin gwamnonin Jihohin Ogun da Osun, Chief Segun Osoba da Chief Bisi Akande, da sauran jiga jigan jam’iyyar APC a ranar Juma’a, 20 ga Nuwamba, sun kaiwa shugaban ƙasa ziyara a fadarsa.

Duk da ba’a bayyana maƙasudin taron ba, George, a martaninsa, ya yi iƙirarin cewa taron anyi shi ne saboda jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, kamar yadda jaridar The Guardian ta rawaito.

Ya ce taron bashi da wata manufa bayan abinda ya bayyana ƙarara duk da akwai ɓoyayyar manufa, inda ya yi iƙirarin cewa rashin ganin fuskar Tinubu yayin taron ya tabbatar an yi taron ne akansa.

Ya ƙara da cewa taron anyi shi ne don “don sauƙaƙawa Tinubu da nemar masa afuwa”.

Jigon na jam’iyyar PDP ya shawarci Buhari a kan kar ya yarda ya faɗa tarkon wanda zasu sauya asalin batun da ke damun jihar Legas domin biyan bukatar kansu da wasu tisararun mutane.

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP ya ce akwai bukatar Tinubu ya biya bashin makudan kudaden da ya wawushe daga aljihun jihar Legas.

A rahoton da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa, ta bayyana cewa George ya yi yunƙurin mamaye siyasar jihar Legas, wanda hakan yasa shi bada gudunmawa ga zanga zangar EndSARS, musamman a Lekki tollgate.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here