Fitaccen Attajiri ya Rasu – Chief Harry Akande
Sanannen dan kasuwa Chief Harry Akande ya rasu a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba.
Ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya kamar yadda dan shi ya sanar a wata takarda.
Fitaccen mai arzikin ya kasance mai fatan tabbatar da zama Najeriya kasa ta gari da adalci.
Fitaccen dan kasuwa kuma tsohon dan takarar kujerar shugabancin kasa, Harry Akande ya rasu.Dan kasuwan ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.
A wata takarda da dan sa mai suna Olumide Akande ya fitar a madadin iyalan, ya ce ya rasu a sa’o’in farko na ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya.
Read Also:
“Chief Harry Akande dan kasuwa ne sananne ba a gida Najeriya kadai ba har da kasashen ketare, yana da rinjaye a nahiyoyin duniya,” takardar tace.
Takardar ta kara da cewa, “abinda ya fi so a rayuwarsa shine ganin Najeriya ta zama kasa ta gari sannan adalci ya tabbata. Yana saka wa a ransa cewa hakan za ta faru babu dadewa.”
An haifa marigayin a ranar 3 ga watan Maris 1943. ya halarci makarantar Olive Heights a Ibadan inda ya samu ilimin sakandare kafin ya tafi Amurka domin didigirinsa na farko da na biyu. Ya dawo Najeriya a shekarun 1970 inda ya fara aiki.
Ya kafa kamfaninsa mai suna Akande International Corporation a 1971, jaridar Thisday ta wallafa.
A fannin siyasa, yana daga cikin jiga-jigan da suka kafa jam’iyyar All Peoples Party (APP) wacce ta zamo jam’iyya ta biyu mafi rinjaye a Najeriya.
Akande ya nemi kujerar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar ANPP daga bisani.