Farkon 2023: Hatsarin Mota ya Hallaka Mutane 871 a Iran

 

Rahotanni da hukumomi suka fitar a Iran, sun bayyana cewa mutum 871 ne suka mutu sakamakon hatsarin mota a farkon wannan shekara.

Mataimakin shugaban ‘yan sandan kula da zirga-zirgar ababen hawa a ƙasar, Birgediya Janar Taimur Hosseini, ya ce haɗuran sun afku ne tsakanin watan Maris zuwa watan Afrilun wannan shekara.

A cewar rahotonnin, kashi 28 na waɗanda lamarin ya rutsa da su sun kasance ƴan kasa da shekara 18, kashi 3 masu tafiya a kafa, kashi 10 masu tuka babura, yayin da kashi 33 kuma suka kasance direbobin ababen hawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here