Rikicin Shugabanci: Ƴan Sanda Sun Rufe Majalisar Dokokin Jihar Filato

 

Rundunar ƴan sandan jihar Filato ta rufe zauren majalisar dokokin jihar kan rikicin shugabanci da ake ci gaba da yi.

Jami’an kwantar da tarzoma sun isa harabar majalisar ne da misalin karfe 5 na safiya, inda suka toshe hanyar shiga majalisar.

Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar kawo yanzu, amma rahotanni na bayyana cewa hakan ba ya rasa nasaba da rikici tsakanin mambobin majalisar kan wanda zai shugabanceta.

Kawunan ƴan majalisar ya rabu gida biyu, inda wasu ke ɓangaren kakakin majalisar na yanzu Rt. Hon Yakubu Sanda yayin da wasu kuma ke goyon bayan kakakin majalisar da aka mayar kan kujerar Rt. Hon Ayuba Abok wanda aka tuɓe a watan Oktoban 2021.

Wata kotu ce ta sake mayar da Abon kan kujerarsa ta shugaban majalisar a ranar Litinin, inda washegari ya yi bayyana a majalisar a matsayin shugaba.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here