Donald Trump ya Koma Gida Bayan Halartar Zaman Kotu

 

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya koma gidansa da ke Mar-a-Lago a Florida, bayan kin amsa tuhume tuhume 34 da a kai masa a kotun New York.

Ana zargin Mr Trump da jirkita bayanai na karya da kuma biyan toshiyar baki domin ɓoye wasu bayanai da za su ɓata masa suna a lokacin zaɓen 2016.

To amma da ya ke jawabi ga magoya bayansa, Mr Trump ya ce laifinsa kawai shi ne da ya tsaya kai da fata ba tsoro wajen kare ƙasarsa daga wajen waɗanda ke son su lalata ta.

A cikin salo irin na yakin neman zaɓe, ya soki gwamnatin Biden tare da nanata cewa an yi masa maguɗi a zaɓen 2020, inda aka kayar dashi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here