Hatsarin Jirgi ya yi Sanadin Kashe Mutane a Mali
Hukumomin soji a Mali sun sanar da rikitowar wani jirgin sama kan gidajen mutane a Bamako babban birnin ƙasar.
Sanarwar da sojin suka fitar ta bayyana cewa jirgin yana kan hanyarsa ta dawowa ne daga wani aiki na yaƙar masu iƙirarin jihadi ne kuma akwai yiwuwar an samu asarar rayuka.
Read Also:
Lamarin na faruwa ne sa’o’i kaɗan bayan an yi wa wani sansanin soji da ke birnin Sevare kwanton ɓauna inda aka kashe akalla mutum 9.
A shekarar da ta gabata rundunar sojin ƙasar Mali ta gayyaci waɗanda ta kira masu ba da horo na soji ‘yan Rasha domin su taimaka wa ƙasar wajen samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Mali ta gayyaci sojojin haya na Wagner ne domin taimaka mata ta yaƙi masu tayar-da-ƙayar-baya.