Sojojin India 7 Sun Rasa Rayukansu Sanadiyyar Hatsarin Mota

Rundunar sojin India ta ce sojojinta bakwai sun mutu bayan da motar da suke ciki ta sauka daga hanya ta fada cikin wani kogi a arewacin yankin Ladakh.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce tawagar sojojin su 26 na tafiya ne a cikin bas a lokacin da hadarin ya afku.

Rahotanni sun ce wadanda suka tsira da ransu a cikin motar sun samu mummunan rauni.

A cikin shekaru biyu da suka wuce an yi wata arangama tsakanin sojojin India da na China inda aka kashe na India 20 na China kuma da dama.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here