Adadin Mutanen da Aka Tilasta wa Barin Gidajensu a Congo
Read Also:
Sama da mutum 37,000 ne aka tilasta wa barin gidajensu a Jamhuriyyar Demokraɗiyyar Congo a cikin kwana huɗu sakamakon rikicin da ake gwabzawa, kamar yadda hukumomin bayar da agaji na ƙasar suka bayyana.
Kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun rawaito cewa sojojin ƙasar sun sake ƙwace iko da wasu wurare waɗanda ƴan tawayen M23 suka ƙwace a ƴan kwanakin nan.