Ricikin Rasha da Ukraine: Kamfanin Barasa na Heineken ya Fice Daga Rasha
Kamfanin da ke samar da barasa na Heineken ya ce ya fice daga Rasha.
Kamfanin ya kasance na baya baya bayan nan daga cikin jerin kamfanonin kasashen Yamma da suka dauki irin wannan mataki sakamakon mamayar da Rashan ke yi a Ukraine.
Read Also:
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce ya kammala dukkan shirye-shiryensa na daina duk wata huldar kasuwanci a Rasha.
Tuni dama kamfanin da dakatar da sayar irin kayayyakinsa dama samar da su a Rasha, sannan ya kuma soke duk wani batu na zuba jari a kasar tun farkon watan da muke ciki.
Akwai kamfanoni da dama da suka janye daga Rasha kamar Ikea da Coca-Cola da kuma MacDonalds.