Hezbollah ta kai Hare-hare Fiye da 60 kan Isra’ila
Ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Lebanon ta ce ta kai hare-hare guda 63 kan Isra’ila a ranar Lahadi.
Read Also:
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Telegram, Hezbollah ta bayyana cewa ta yi amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa, da kuma harbin manyan bindigogi wajen kai hare-haren kan sojojin Isra’ila, a cikin Isra’ila da kuma kudancin Lebanon.
Dangane da barazanar da Hezbollah ke yi, Isra’ila ta ƙaddamar da farmakin ƙasa a kudancin Lebanon.
Tun daga ranar 1 ga watan Maris, hare-haren Isra’ila a Lebanon sun yi sanadin mutuwar mutane 1,029, tare da jikkata 2,786, yayin da sama da mutum miliyan guda suka rasa matsugunansu.















