Kungiyar Hisbah ta Kama Mabarata 178

 

Gwamnatin jihar Kano ta haramta wa mutane fita kan ttiti suna yawon bara.

Shugaban dakarun Hisbah, Malam Harun Ibn-Sina ya ce ana kama masu laifi.

Anyi ram da wasu dake wannan haramtaccen aiki, kuma ana cigaba da kame.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mutane 178 da ake zargi da laifin yin bara a cikin birnin jihar, jaridar Vanguard ta bayyana wannan.

Shugaban dakarun Hisbah, Malam Harun Ibn-Sina ya bayyana wannan a lokacin da ya yi hira da hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN.

Da yake magana da ‘yan jarida a yau, ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, 2020, Harun Ibn-Sina ya yi karin haske a game da jama’an da suka kama.

“An kama wadanda ake zargi da laifi ne a lungun Alu Avenue, Dan’agundi, Taludu, Unguwar Race Course, Sharada, Kofar Mazugal a cikin birni.”

Daga cikin wadanda suka shiga hannun hukumar akwai mata 100 da maza 76 inji Ibn-Sina.

Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauki matakin hana bara a jihar Kano, wanda wannan ya jawo surutu tsakanin masu tir da goyon-bayan tsarin.

Ya ce: “An rage bara a titi a jihar tun da hukuma ta shiga aikin neman farautar masu saba doka.”

“Hukumar za tayi kokarin ganin babu ragowar mai bara a jihar Kano nan gaba.” Harun Ibn-Sina yace gawurtattun wadanda aka kama zasu yaba wa aya zaki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here