AMCON: Shugaba Buhari ya sake Zaben Ahmed kuru a Matsayin Manajan Darekta

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wasu muhimman nade-nade a hukumomin NDIC da AMCON.

Sanar da sabbin nade-nade na kunshe a cikin sanarwar da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar ranar Litinin.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sake zaben Ahmed Kuru a matsayin manajan darekta a hukumar kula da kadarori ta kasa (AMCON).

Kazalika, ya amince da nada Eberechukwu Uneze da Aminu Isma’il a matsayin darektoci ma su cikakken iko na zangon wa’adin shekaru biyar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Litinin.

A cewar Garba Shehu, shugaba Buhari ya aika sunayen mutanen zuwa majalisar dattijai domin neman amincewarta.

Kazalika, shugaba Buhari, a cikin wata wasikar daban, ya nemi majalisar dattijai ta amince da nadin Mista Bello Hassan a matsayin manajan darekta a hukumar NDIC.

A cikin wasikar, Buhari ya nemi majalisar ta amince da nadin Mustapha Muhammad Ibrahim a matsayin darektan mai cikakken iko a hukumar.

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here