Titin Abuja-Kaduna: Hukumar Mayakan Saman Najeriya ta Gudanar da Atisayen Ceto Mutane

Titin Kaduna zuwa Abuja ta yi kaurin suna da yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Lokuta bila adadin, an yi garkuwa da yan Najeriya da dama, ciki har da jami’an tsaro.

Hafshoshin sojin sama sun gudanar da atisayen taimakawa wajen ceto a titin.

Hukumar mayakan saman Najeriya NAF ta gudanar da atisayen na musamman kan yadda ake ceto mutane a titin Kaduna zuwa Abuja.

An gudanar da atisayen ranar Asabar, 2 ga watan Junairu, 2021 domin horar da jami’an hukumar kan yaki a kasa.

An gudanar da atisayen mai take “Taimako yazo” a titin Kaduna-Abuja. Kakakin hukumar NAF Air Vice Marshal Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan a shafin hukumar na Tuwita.

A jawabin da yayi, babban hafsan sojin saman, Air Marshal Sadiq Abubakar, yace horar da jami’an hukumar na da muhimmanci domin samun nasara wajen yaki da ta’addanci.

Yace: “Gaba daya manufarmu shine tabbatar da cewa jami’anmu sun kware wajen artabu (da makiya).”

“Hakazalika, atisayen yau wanda aka gudanar kan yadda ake lalube da ceto mutane an yi shi domin inganta kwarewan jami’anmu wajen ceto abokan aikinsu da suka sauka daga cikin jiragensu domin wani aikin gaggawa.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here