Hukumar Sojoji ta Karama Wani Sanannan Marigayin Soja

Bayan watanni biyu a rashinsa, hukumar Sojin Najeriya ta karrama Jarumi Kanal Bako.

Kanal Bako ya rasa rayuwarsa ne a faggen fama a Arewa maso gabas.

Gwamnan jihar Borno ya yi alhinin mutuwar Kana; Bako kuma yi yiwa iyalansa alkawari.

Hukumar Sojin Najeriya ta amince da karawa Marigayi Kanal Dahiru Bako matsayi zuwa Birgediya Janar domin karramashi bisa sadakarwan da yayi, Murtala Abdullahi na jaridar HumAngle ya ruwaito.

Janar Bako ya rasa rayuwarsa sakamakon yaki da Boko Haram kuma an sanar da mutuwarsa bayan aikin da akayi masa a asbiti a Satumba.

Kungiyar ISWAP, wata ballin Boko Haram ce ta kai wannan hari. Kanal Bako wanda ya kasance Birgad Kwamandan na 25 Task Force ya na zaman aikinsa a karamar hukumar Damboa, kilomita 85 zuwa Maiduguri, birnin jihar Borno.

Ya kasance Soja a ake matukar girmamawa bisa jaruntarsa da jagorantan Sojoji zuwa faggen dama har da daji mai hadari, Algarno.

“Ya yi yaki sosao. Ya kawar da makiya zaman lafiya kuma ya kare rayukan mutan jihar Borno har sai da ya sadaukar da rayuwarsa yana karesu” cewar gwamnan jihar Borno, Babagana zulum.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya cika alkawarinsa na kyautan naira milyan ashirin da ya yiwa iyalan jarumin kwamandan da aka kashe a filin yaki da yan ta’addan Boko Haram.

Gwamnan ya sanar da hakan da safiyar Laraba, a shafinsa na Tuwita da Facebook. A ranar Litinin ne rundunar soji ta Najeriya ta sanar da mutuwar Kanal D. C. Bako, kwamandar runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Bayan Kanar Dahiru Chiroma Bako da aka kashe, Zulum ya sanar da baiwa iyalan sauran Sojoji uku da aka kashe tare da shi milyan biyu-biyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here