Hukuncin da Kotu ta Yanke wa Matar da ta ke Bincike Wayar Mijinta ba Tare da Izini ba
Wata kotu ta yanke wa wata mata hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata uku bisa zargin keta sirrin mijinta.
Matar dai tana ɗaukar wayar maigidanta domin binciken abinda yake aikatawa, shi kuma ya maka ta a Kotu.
A cewarta ta yi hakane saboda zargin da take masa na cin amanarta da wayar.
United Arab Emirate – Wata kotu a haɗaɗɗiyar dauƙar Larabawa (UAE) ta yankewa wata mata hukuncin zaman gidan kaso na tsawon wata uku saboda duba wayar mijinta ba tare da izini ba.
Read Also:
Aminiya Hausa ta rahoto cewa mijin ya kai ƙarar matar ne gaban kotu, domin a bi masa haƙƙinsa na duba wayarsa da take yi ba tare da neman izini ba.
Rahotanni sun bayyana cewa kotun dake zamanta a yankin Ras a Al-Khaima ta kama matar dumu-dumu da laifin keta sirrin mijinta.
Matar zata biya tarar kuɗi
Hakanan kuma kotun ta tuhumi matar da laifukan kwafar bayanan mijinta, hotuna da sauran wasu mu’amalansa ta hanyar amfani da wasu manhajoji.
Bayan tabbatar da laifin matar, kotun ta yanke mata hukuncin biyan tarar kuɗi da suka kai kimanin AED 8,100.
Meyasa matar take duba wayar maigidanta?
A ɓangarenta, matar ta bayyana cewa tana duba wayar maigidanta ne saboda tana zarginsa da cin amanarta.
Ana ganin dai UAE na kan gaba wajen kafa dokoki masu tsauri, musamman waɗanda suka shafi mu’amalar aure da zamantakewa ta yau da kullum.