Nuna Rashin da’a: Ingila za ta Buga Wasa Babu ‘Yan kallo

 

Ingila za ta buga wasa daya ba tare da yan kallo ba a matsayin hukuncin nuna rashin da’a da magoya bayanta suka nuna a wasan karshe na Euro 2020 da aka yi a filin wasa na Wembley.

Hukumar shirya kwallon kafa ta Turai wato UEFA ta kuma ci tarar tawagar Three Lions fam 84,560.

Sai dai a martanin da ta yi, hukumar kwallon kafa ta Ingila ta nuna rashin jin dadinta da hukuncin na UEFA, amma kuma duk da haka ta ce ta yi na’am da shi.

Yan kallo sun rika fada da masu kula da filin Wembley da kuma yan sanda, a kokarinsu na shiga filin wasan ta karfi a ranar 11 ga watan Yuli, inda Ingila ta yi rashin nasara a wasan na karshe a hannun Italiya.

Lamarin ya sa wasu yan kallo sun jikkata, da suka hada da mahaifin kyaftin din Ingila kuma mai tsaron bayan Manchester United Harry Maguire.

Kuma a lokacin yan sandan Burtaniya suka sanar da kama mutun 51.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here